2020-01-15 13:48:12 cri |
A bikin na wannan karo, an kirkiro sabbin shirye-shirye da hanyoyin gwada shirye-shirye. An kuma kafa dandalin watsa bikin a birnin Beijing, da birnin Zhengzhou dake lardin Henan, da yankin Guangdong da Hong Kong da Macau, inda za a gabatar da shirye-shiryen wasan kwaikwayo ban dariya, da wake-wake da raye-raye, da wasan kwaikwayo na gargajiya, da wasan dabo da sauransu. Ban da wannan kuma, za a yi amfani da sabuwar hanyar gwada shirye-shirye, don baiwa masu kallo damar da su shiga shirye-shirye tare, ta hakan za a gabatar da gagarumin biki mai gamsar da jama'a sosai.
Bikin murnar ranar bikin bazara biki ne dake gwada al'adun Sinawa, za a fara bikin ne a ranar 24 ga wannan wata. (Zainab)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China