Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na kan gaba wajen yawan samar da motoci masu amfani da sabbin makamashi
2020-01-13 13:29:59        cri

Ministan kasar Sin mai kula da masana'antu da sabbin fasahohin sadarwa Miao Wei, ya furta a wajen wani taron sana'ar samar da motoci masu amfani da wutar lantarki, wanda ya gudana a kwanakin baya a birnin Beijing cewa, yawan motoci masu amfani da sabbin makamashi da kasar Sin ta samar, gami da sayar da su a shekarar 2019, sun wuce miliyan 1.2, adadin da ya zama kan gaba a duk duniya.

A cewar ministan kasar Sin, kasarsa ta dade tana cikin wani yanayi mai kyau, a fannin raya harka mai alaka da motoci masu amfani da sabbin makamashi. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China