Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a watsa bikin murnar sabuwar shekarar kasar Sin ta fasahar 8K
2020-01-14 13:48:46        cri

Babban rukunin gidajen rediyo da telibijin kasar Sin CMG ya yi bikin gabatar da fasahohin 5G da 8k ko 4k da kuma VR, wadanda za a yi amfani da su wajen gabatar da bikin raye-raye da wake-wake na murnar sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiya a yau Talata a cibiyar watsa labarai ta Media Center dake nan birnin Beijing.

An ba da labari cewa, ya zuwa yanzu, 5G ta karade filayen daban-daban na bikin. Kuma CMG zai yi amfani da fasahohin 5G da 8k wajen daukar shirye-shiryen bikin da hotunan bidiyo daga bangarori daban-daban, da kuma gabatar da shirye-shiryen kai tsaye ta yin amfani da na'urori na zamani. Ban da wannan kuma, wannan shi ne karo na farko da za a yi amfani da tsarin VNIS yayin bikin, wato yin tuntuba tsakanin mutane ta hanyar kallon shirin ta fasahar VR. Duk wadannan matakai za su baiwa masu kallo damar shakatawa da more gaggarumin biki ta fasaha da kimiyyar zamani wato 5G da 8k ko 4k da VR. da kuma sabuwar kafar kallon shirye-shirye (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China