Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Zambia ya ce ba za'a laminci wasu daga ketare su dinga mulkar Afrika ba
2020-01-14 10:19:12        cri
Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu ya ce ba za'a yarda wasu daga ketare su dinga bada umarnin yadda za'a tafiyar da shugabanci a kasashen Afrika ba.

Lungu ya ce, kamata ya yi a kyale Afrika ta gudanar da harkokin mulkinta da kanta maimakon wasu daga ketare su dinga tsara yadda za'a tafiyar da shugabancin kasashen.

Ya ce sannu a hankali Afrika ta fara zabar hanyar da za ta shugabanci al'ummarta da irin tsarin shugabancin da ya dace da yanayin da al'ummar ke ciki, kamar yadda gidan talabijin na kasar ya ambato shugaban kasar na bayyanawa.

A tsokacin da ya yi lokacin da jakadan Sudan a kasar Zambiya mai barin gado, Award Ali, ya ziyarce shi, shugaban kasar ta Zambia ya ce, gwamnatinsa a shirye take ta hada kai da dukkan bangarorin shugabannin shiyyoyin Afrika.

A cewarsa, kasashen Afrika za su samu ci gaba ne kadai idan suka yi la'akari da muhimman bukatun da suke da shi kana suka yi aiki tukuru wajen cimma nasarar bunkasuwar su. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China