Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin kasar Sin ya tallafa a yakin da ake yi da karancin abinci a Zambia
2019-09-30 11:35:04        cri
Kamfanin hadin-gwiwar kasa da kasa ta fannin tattalin arziki da fasaha na lardin Jiangxi na kasar Sin wato China Jiangxi International Economic Technical Cooperation a turance, ya bayar da tallafin kudi da yawan su ya kai kimanin dalar Amurka 75,470 ga gwamnatin Zambia, a matsayin gudummawarsa ga yakin da kasar ke yi da kamfar abinci.

Kakakin hukumar yaki da bala'u a kasar Zambia Rachel Chama, ya ce tallafin kamfanin zai taimaka matuka, wajen dakile tasirin kamfar abinci, wadda ta biyo bayan fari da karancin yabanya da suka shafi wasu sassan kasar.

Cikin wata sanarwa, Mista Chama ya ce kamfanin na Sin ya mika cakin kudin tallafin ga mataimakiyar shugaban kasar ta Zambia Inonge Wina, yayin wani biki da aka gudanar a ranar Asabar.

Da take karbar tallafin, madam Inonge Wina, ta jinjinawa kwazon wannan kamfani, wanda ya nuna irin tausayi da jin kai da mahukuntansa ke da shi, lamarin da ke nuni ga kyakkyawar dangantakar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Zambia. Daga nan sai ta sha alwashin yin amfani da kudaden ta hanyar da ta dace, wadda za ta amfani al'ummun da matsalar ta fi shafa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China