Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bukaci kasashen Afrika su ci gaba da karfafa dangantakarsu da kasar Sin
2019-09-29 16:44:29        cri
An bukaci kasashen Afrika su ci gaba da kokarin karfafa dangantakarsu da kasar Sin, domin ita ce hanyar da ta dace na inganta ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

Lawarence Banda, mataimakin Sakatare Janar na Kungiyar dake rajin wanzar da zaman lafiya a duniya ta Universal Peace Federation, reshen kasar Zambia, ya shaidawa Xinhua cewa, kasar Sin ta nuna ta hanyoyi da dama cewa, ta kuduri niyyar taimakawa nahiyar Afrika, wajen cimma burikanta na ci gaba, tare kuma da inganta zaman lafiya a duniya.

Lawrence Banda, ya yi kira ga gwamnatocin Afrika su yi kokarin zurfafa dangantakarsu da kasar Sin ta hanyar musayar al'adu da cudanya tsakanin jama'arsu da kuma cinikayya.

Ya bada misali da jerin ayyukan more rayuwa da kasar Sin ta taimaka wajen aiwatarwa a Afrika da kuma manufar bude kofa da gyare-gyare ta kasar Sin, wadda ta kai kayayyakin nahiyar Afrika kasuwar kasar Sin.

Ya ce a bayyane yake cewa, ababen more rayuwa su ne jigon ci gaban tattalin arziki, kuma kasar Sin ta dade tana taimakawa nahiyar da ayyukan more rayuwa.

Bugu da kari, ya ce kasar Sin ta nuna cewa, za a iya samun ci gaban tattalin arziki tare da fitar da miliyoyin mutane daga kangin talauci a cikin wasu 'yan shekaru. Yana mai cewa, wannan kadai gagarumin darasi ne ga Afrika, sannan yana ba nahiyar kwarin gwiwa samun ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China