Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zambia ta tanadi wadataccen abinci ga jama'ar yankunan dake fama da matsalar yunwa
2019-10-22 10:10:43        cri
Gwamnatin kasar Zambiya ta tabbatar a jiya Litinin cewa, kasar ta yi kyakkyawan tanadin kayan abinci domin rabawa jama'ar yankunan kasar da matsalar yunwa ta shafa.

Kimanin yankunan kasar 58 ne suka fada cikin yanayin karancin abinci sakamakon matsalar tangardar damina da suka samu. A halin yanzu kusan mutane miliyan 2.3 a kasar ne suke cikin yanayin bukatar tallafin abinci.

Chanda Kabwe, shugaban hukumar yaki da bala'u na kasar ya ce, babu bukatar al'ummar kasar su ta da hankulansu kasancewar gwamnati ta yi kyakkyawan tanadin daidaita matsalar.

Jami'in ya bayyana hakan ne a lokacin wata hira da ya yi kai tsaye ta shirin gidan Radiyon Pan African yana mai cewa, babu wanda zai mutu saboda yunwa kuma gwamnatin kasar ta shirya tsab don rarraba kayan tallafin abinci ga al'ummar kasar.

Sai dai ya zargi wasu masu ruwa da tsaki da yunkurin siyasantar da al'amarin, inda suke yada labarun bogi game da halin da ake ciki, suna cewa yunwa ta kashe mutane a wasu yankunan kasar.

A cewarsa, tuni hukumar ta tanadi ton 5, 000 na wake domin rabawa jama'ar dake cikin yanayin bukatar tallafin, kana hukumar tana ci gaba da kokarin sayo karin kayan abinci don rarraba shi ga mabukata. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China