Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara sa ido kan ayyukan kawar da talauci
2020-01-13 21:16:39        cri
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada cewa, a shekarar da muke ciki, za a dora muhimmanci kan wasu manyan matsaloli masu lahanta moriyar jama'a, dake yankuna masu fama da talauci, da kara sa ido kan sakamakon ayyukan kawar da talauci, musamman ma a gundumomi masu fama da talauci.

Shugaban na Sin, ya bayyana hakan ne a yayin taron shekara ta 2020, na kwamitin ladabtarwar kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, yana mai cewa, za a murkushe cin hanci a fannin zaman rayuwar jama'a, da wadanda ke goyon bayan muggan kungiyoyi dake aikata ta'addanci, da masu kawo cikas ga tabbatar da manufofin samar da alheri ga jama'a, don inganta hukumomin jam'iyyar dake kananan hukumomi, ta yadda za su gudanar da ayyuka yadda ya kamata a dukkan fannoni. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China