Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya karrama masana biyu da lambobin yabo mafi girma na kasar Sin a fannin kimiyya
2020-01-10 15:38:39        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mikawa Huang Xuhua da Zeng Qingcun lambar yabo mafi girma ta kasar Sin a fannin kimiyya a yau Jumma'a, bisa babbar gudummowar da suka bayar a fannin kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya da fasaha a kasar Sin.

Shugaba Xi Jinping ya mika lambobin yabon girmamawa da takardun shaida ne a yayin wani biki da aka shirya a Beijing don karrama mutanen da suka yi fice a fannonin kimiyya, da fasaha, da kuma bincike.

Huang Xuhua, kwararre daga kwalejin nazarin injiniya na kasar Sin, kana babban masanin tsara jiragen ruwan yaki na karkashin ruwa masu amfani da nukiliyar kasar Sin na farko.

Zeng Qingcun, ya kasance kwararren masani ne daga kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin (CAS), shahararren masanin hasashen yanayi na sararin sama na cibiyar nazarin samarin samaniya dake karkashin kwalejin ta CAS. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China