Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya jaddada bukatar bincike da sanya ido kan masu rike da madafun iko
2020-01-13 20:53:42        cri
Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da bincike, da sanya ido kan masu rike da madafun iko, a gabar da yake jaddada muhimmancin dorewar managarcin tsarin gudanar da JKS.

Shugaba Xi, wanda kuma shi ne shugaban hukumar koli ta rundunar sojojin kasar ta Sin, ya yi wannan tsokaci ne, cikin jawabin sa a wajen cikakken zaman taro na hudu, na kwamitin ladabtarwar JKS, karo na 19 da ya gudana yau Litinin a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China