Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya amsa tambayoyin manema labarai game da zaben Taiwan
2020-01-12 17:15:24        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya amsa tambayoyin manema labarai game da zaben da aka yi a yankin Taiwan, inda ya ce, kakakin ofishin kula da batun Taiwan na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis da ofishin kula da batun Taiwan na majalisar gudanarwa ya riga ya yi sharhi kan sakamakon zaben. Geng ya ce, batun yankin Taiwan, batu ne na cikin gidan kasar Sin. Duk da canzawar halin da ake ciki a Taiwan, akwai wani abun da ba zai taba canzawa ba, wato akwai kasar Sin daya tak a duk fadin duniya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar.

Gwamnatin kasar Sin tana tsayawa kan manufar kasancewar kasar daya tilo a duniya, tana kuma kin yarda da ballewar Taiwan daga cikinta, da kin yarda da "kasancewar kasar Sin biyu" da "kasancewar kasar Sin daya da Taiwan daya" a duniya. Haka kuma kasashen duniya ba zasu sauya matsaya daya da suka cimma ba wato kasancewar kasar Sin daya tak a duniya.

Geng ya kara da cewa, ana fatan kasashen duniya zasu ci gaba da goyon-bayan manufar gwamnatin kasar Sin ta kasancewar kasa daya tak a duniya, da nuna fahimta gami da marawa al'ummar kasar baya wajen kin yarda da duk wani yunkuri na ballewar Taiwan daga kasar Sin, da cimma muradun dinke kasar Sin baki daya tun da wuri.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China