Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta janye shirinta na sayarwa yankin Taiwan makamai
2019-07-09 20:17:33        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Geng Shuang ya bayyana cewa, kasarsa ta bukaci Amurka da ta gaggauta janye shirinta na sayarwa yankin Taiwan makamai da ma alakar soja dake tsakaninta da yankin.

Geng wanda ya bayyana hakan a Talatar nan yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing, ya ce, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya da sanarwowi guda uku game da alakar Sin da Amurka, ta hanzarta janye shirinta na sayarwa yankin makamai da ma huldar soja tsakaninta da yankin na Taiwan don kaucewa kara dagula alaka tsakanin kasashen biyu, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin Taiwan.

Geng ya yi wadannan kalamai ne, yayin da ya ke mayar da martani, ga shirin Amurka na sayarwa yankin na Taiwan makamai da darajarsu ta kai biliyan 2.2, ciki har da tankokin yaki samfurin M1A2 Abrams da na'urorin kakkabo makamai masu linzami.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China