Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na matukar adawa da hulda tsakanin Amurka da Taiwan
2019-05-28 10:55:52        cri
Kasar Sin ta furta adawarta da kakkausar murya kan hulda kowacce iri bisa kowane yanayi tsakanin Amurka da Taiwan a hukumance.

Yayin wani taron manema labarai a jiya, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Lu Kang, ya ce kasar Sin ba ta gamsu ba, kuma ba ta amince da hulda tsakanin Amurka da Taiwan ba.

Rahotanni na cewa, Taiwan ta yi ikirarin mashawarcin shugaban Amurka kan harkokin tsaro, John Bolton ya tattauna a baya bayan nan da takwaransa na Taiwan.

A martanin da ya mayar, Lu Kang ya ce gwamnatin Amurka na sane cewa, gwamnatin Jamhuriyar Al'ummar kasar Sin ita ce halaltacciyar gwamnati daya tilo dake wakiltar baki dayan kasar Sin, kuma ta yi alkawarin ba za ta yi wata hulda da Taiwan ba. Don haka, ba yadda za a yi John Bolton da David Lee su kasance masu mukami iri guda.

Ya kara da cewa, manufar kasar Sin daya tak a duniya, ita ce tubalin huldar Sin da Amurka, kuma gwamnatin Sin na matukar adawa da yunkurin kirkirar "kasashen Sin 2", ko kuma "kasar Sin da Taiwan". Mr. Lu Kang yana mai cewa, matsayar gwamnatin kasar Sin a bayyane take, kuma ba za ta sassauta ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China