Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko kadan Sin ba ta yarda da shirin Amurka na sayarwa yankin Taiwan makamai ba
2019-08-17 16:26:07        cri
Game da yadda gwamnatin Amurka ke shirin sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin jiragen saman yaki kirar F-16V wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 8, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana a ranar 16 ga wata cewar, yunkurin Amurka na sayarwa Taiwan makamai ya sabawa manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya da kuma sanarwoyi uku da Sin da Amukra suka bayar cikin hadin gwiwa, lamarin ya shafi tsoma baki ne kan harkokin cikin gidan kasar Sin, da lalata ikon mulkin Sin, da muradunta ta fuskar tsaro, don haka Sin ta nuna rashin yardar da kakkausan harshe, kuma ta riga ta nunawa Amurka rashin jin dadinta.

Ban da wannan kuma, Madam Hua ta jaddada cewa, batun Taiwan na da nasaba da ikon mulkin kasar Sin da cikakkun yankunan kasar da ma babbar moriyar kasar. Hua ta ce, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta fahimci sarkakiyar dake tattare da batun da ma babbar illar da batun zai haifar, da bin manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya da ma abubuwan da aka tanada cikin sanarwoyi uku. Bugu da kari, Sin ta kalubalanci Amurka da ta daina sayarwa Taiwan jiragen saman yaki kirar F-16V gami da dakatar da batun sayar mata makamai da ma tuntubarsu ta fuskar aikin soja. Idan ba haka ba, dole ne Sin za ta mayar da martani mai tsanani, Amurka kuwa za ta dauki dukkan alhakin sakamakon da batun zai haifar. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China