Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka shiga ko suka fita daga Sin a shekarar 2019 ya kai miliyan 670
2020-01-06 16:00:59        cri
Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin baki ta kasar Sin ta gabatar a kwanakin baya, an ce, yawan mutanen da suka shigo ko suka fita daga Sin a shekarar 2019 ya kai miliyan 670, adadin da ya karu da kashi 3.8 cikin dari.

A shekarar 2019, an kafa hanyoyin bincike guda 89 a birnin Beijing, da Shanghai, da sauran wuraren kasar Sin da yawansu ya kai 18, wadanda suka samar da sauki ga mutane dubu 290 na kasashe masu bin shawarar "ziri daya da hanya daya", da mutane daga kasashen da suke shigowa kasar Sin.

Kana an gabatar da manufofin shiga kasar Sin ba tare da samun takardar visa na tsawon kwanaki 30 a tsibirin Hainan na kasar Sin, wanda hakan ya kawo moriya ga kashi 7 cikin goma na mutane daga kasashen ketare, da suka shigo Sin ta tsibirin Hainan. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China