Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan mutanen da suka je yawon shakatawa a lokacin kankara ya kai fiye da miliyan 224
2020-01-07 13:16:22        cri

Ofishin nazarin yawon shakatawa na kasar Sin ya fitar da wani rahoto mai suna "Rahoton bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa a lokacin kankara na shekarar 2020" wanda ya nuna cewa, yawan mutanen da suka je yawon shakatawa a lokacin kankara na shekarar 2018 zuwa 2019, ya kai fiye da miliyan 224, yawan kudin da aka samu a wannan fanni ya zarce Yuan RMB bilyan 380, lamarin da ya nuna cewa, bangaren na ci gaba da samun bunkasuwa cikin sauri. An yi kiyasin cewa, ya zuwa shekarar 2022, lokacin da za a gudanar da wasan Olympic na lokacin sanyi, yawan mutanen da za su je yawon shakatawa zai kai fiye da miliyan 340, yawan kudin shigar da za a samu kuma, zai kai Yuan RMB biliyan 680. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China