Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana shirin harba sama da taurarin dan-Adam 40 a shekarar 2020
2020-01-03 15:51:52        cri
Hukumar nazarin kimiya da fasahar kere-kere sararin samaniya ta kasar Sin (CASC) ta bayyana cewa, sashen zirgar-zirgar sararin samaniyar kasar, zai gudanar da ayyuka da dama a shekarar 2020, inda ya ke fatan harba taurarin dan-Adam da suka zarce 40.

Daga cikin ayyukan da hukumar za ta gudanar, sun hada da harba nau'rar bincike duniyar Mars na farko da kasar ta Sin za ta yi, da kumbon bincike na Chang'e-5, wanda ake sa ran zai dauko samfura daga duniyar wata zuwa doron duniya, da matakin kasar na karshe game da shirin binciken sararin samaniya dake gudana, gami da kammala tsarin shawagin tauraron dan-Adam na Beidou.

Hukumar CASC ta ce. Sabbin rokokin harba taurarin dan Adam guda uku da za a yi amfani da su a shekarar ta 2020, sun hada da Long March-5B, Long March-7A da Long March-8

Bugu da kari, za a harba wasu taurarin dan-Adam na kasuwanci kamar tauraron dan-Adam na APSTAR-6D. Haka kuma za a harba taurarin dan-Adam da za a yi amfani da shi wajen samar da intanet.

Yawan taurarin dan-Adam din da kasar Sin ta harba a cikin shekaru biyu da suka gabata, ya sanya ta zama kan gaba a duniya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China