Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta yi hasashen rage hakar danyen mai a shekarar 2020
2019-12-20 09:05:01        cri
Gwamnatin Najeriya ta yi kiyasin hako gangar danyen mai miliyan 2.18 a kowace rana wato (MBPD), a cikin kunshin kasafin kudin kasar na shekarar 2020, gwamnatin tana ganin hakan shi ne zai fi zama tabbas.

Ministar kudi da tsare tsaren kasa da kasafin kudi ta Najeriyar, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan a Abuja, babban birnin kasar, ta ce wannan yayi kasa da hasashen ganga miliyan 2.3 MBPD a shekarar 2019.

Ta ce hakikanin danyen man da kasar ke hakowa da fitar da shi ketare yana raguwa kasa da abin da ake hasashe a kasafin kudin kasar tun daga shekarar 2013 duk da kasancewar kasar tana da karfin hako ganga miliyan 2.5 a kullum sakamakon wasu tarin dalilai.

Ministar ta ce a shekarar 2018, hakikanin MBPD miliyan 1.84 ake hakowa a kullum, kana a watanni shidan farkon shekarar 2019 ana hakar ganga miliyan 1.86 MBPD.

A cewarta, kasafin kudin kasar ya yi kiyasin farashin gangar danyen mai a kan dala 57 kana hawa-hawar farashi kashi 10.81 bisa 100.

Ministar ta kara da cewa, ana hasashen karuwar tattalin arzikin GDP a kasar da kashi 2.93 bisa 100, sama da kashi 2.4 bisa 100 kamar yadda bankin raya kasashen Afrika ya yi hasashe.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China