Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karfin tuwo zai tsananta halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya
2020-01-04 17:08:30        cri
Ma'aikatar tsaron kasar Amurka ta tabbatar da cewa, babban kwamandan rundunar sojan IRGC ta Iran wato Qasem Soleimani ya mutu a sakamakon harin da sojojin kasar suka kai a ranar 2 ga wata. Jagoran addini na kasar Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya sanar da cewa, kasarsa za ta mayar da martani. Lamarin ya kara tsananta dangantakar dake tsakanin Amurka da Iran, da kawo babbar illa ga halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya.

An yi nuni da cewa, matakin kasar Amurka martanin ne da kasar Amurka ta mayar, dangane da harin da aka kai a ofishin jakadancinta dake kasar Iraki, tare da nuna karfi ga kasar Iran. Amma a bangaren Iran, idan aka kai mata hari, to za ta mayar da martani. Kuma mai yiyuwa kasar Iran ta mayar da martani ta wata hanya ta musamman, wadda ka iya kawo illa ga tsaron muhimmiyar hanyar jigilar makamashi ta teku wato mashigin tekun Hormouz. Kana mutuwar Soleimani za ta kara kawo cikas ga daidaita batun nukiliyar kasar.

An jaddada cewa, zaune tsayen da aka samu a yankin gabas ta tsakiya a dogon lokaci ya shaida cewa, nuna karfin tuwo zai mayar da hannu agogo baya, kana za a tsananta halin da ake ciki. Matakin da kasar Amurka ta dauka ya sa kaimi ga taka hanyar tada rikice-rikice a fili a tsakaninta da Iran, babu shakka za a kara tsananta yanayin yankin gabas ta tsakiya. Ya kamata bangarori daban daban da abin ya shafa musamman kasar Amurka, su kwantar da hankali, da bin ka'idojin tsarin mulkin MDD da ka'idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, ta hakan za a magance tsanantar yanayin yankin, da kuma tabbatar da zaman lafiya da na karko. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China