Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu kafofin watsa labaran yammacin kasashe suna tsara labaran Sin tamkar tsara tatsuniya, in ji shugaban CMG
2020-01-02 14:08:56        cri

Jiya Laraba 1 ga watan Janairu, kafar yada labarai ta kasar Amurka wato U.S. Commerce News ya wallafa wani sharhi mai taken "Wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya suna wallafa labarai game da kasar Sin tamkar tatsuniya, in ji shugaban CMG", cikin sharhin, an ce, jawabin murnar sabuwar shekarar 2020 da shugaban babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin na CMG Shen Haixiong ya gabatar, ya yi bayani kan hadin gwiwa da mu'amalar da ya yi tare da takwarorinsa na kafofin watsa labarai na kasa da kasa kimanin guda 150 cikin shekarar 2019 da ta gabata, ya kuma yi zargin cewa, wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya su kan watsa labaran karya masu cike da jita-jita game da kasar Sin, lamarin da ya keta babbar ka'idar aikin watsa labarai

Sharhin ya kuma bayyana cewa, hukumomin gwamnatin kasar Sin da kafofin watsa labaran kasar sun sha zargin kafofin watsa labarai na kasashen yammacin duniya kan yadda suke yada labaran game da batun Hong Kong, da na kabilar Uygur na jihar Xinjiang na kasar Sin.

Haka kuma jawabin da Shen Haixiong ya gabatar, ya sake jaddada cewa, ya kamata mu yi amfani da damar da fasahar harkokin yanar gizo ta ba mu, da na kirkire-kirkire, ta yadda za a raya CMG zuwa kafar yada labaran da babu kamar ta a duniya.

Haka kuma, jawabin Shen Haixiong ya jaddada cewa, ya kamata mu watsa labaran duniya bisa ka'idojin nuna adalci da gaskiya, da kawar da sabani da kuma daina nuna bambancin ra'ayi ga wani ko wata. Lamarin da ya nuna cewa, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin na CMG ya riga ya zama kafar watsa labaran da ta ci gaba a duniya, a maimakon kafar watsa labarai wadda take mai da hankali kan harkokin Sin kawai. Hakan ya sa, za a sami sabon canji a harkokin watsa labarai a duniya (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China