Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakiliyar CMG ta yi hira da takwarorinta na CNBC
2019-09-05 18:12:13        cri

Ranar 3 ga wata bisa agogon wurin, wakiliyar babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG madam Liu Xin, ta yi hira da masu gabatar da labarai 3 na kasar Amurka, cikin wani shiri da gidan telibijin CNBC na Amurka ya watsa, wanda ya yi suna sosai a duniya wajen watsa labaru masu alaka da hada-hadar kudi da tattalin arziki.

Dukkan wadannan masu gabatar da labarai na Amurka 3, sun gwanance wajen kasancewa a matsayin manema labaru. Don haka dukkan mutanen 4 sun yi fintikau wajen gudanar da hirarraki a gaban masu kallon shirye-shiryen telabijin.

Bayan daukar shirin, madam Liu Xin ta ce, kowa na da ra'ayinsa kan hulda da ke tsakanin Sin da Amurka. Ta kuma taimaka musu wajen kallon kasar Sin ta wata sabuwar hanya, wato hanyar da al'ummar Sin suke bi, ta yadda za su iya kara kallon kasar Sin bisa sanin ya kamata, kuma daga dukkan fannoni. Kowa dai na iya fahimtar cewa, yin mu'amala fuska da fuska zai iya taimaka sosai wajen fahimtar juna.

Watakila ma dai haka lamarin yake, dangane da takaddamar da ke tsakanin Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Kuma tuntubar juna cikin sahihanci ce kadai za ta daidaita wannan matsalar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China