Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jawabin murnar sabuwar shekarar 2020 na shugaban CMG
2020-01-01 16:02:52        cri


Ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2020, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da telibiji na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabin ta rediyo da Intanet ga masu kallo da sauraro dake ketare, ga cikakken jawabinsa:

Abokai da aminai:

Shekarar 2020 wata alkaluma ce mai cike da sa'a, ma'anar sautin wannan shekara a Sinanci ita ce, ina son ka (ki). Albarkacin wannan sabuwar shekara, a madadin CMG, ina muku fatan alheri daga nan birnin Beijing.

Tarihin bil Adama na kunshe da labarai da dama. Kuma wasu abubuwan da suka faru a shekarar 2019 sun shiga kundin tarihi da ba za a iya mantawa da su ba. Alal misali, ran 1 ga watan Oktoba, mun yi murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin. Abokanmu sun shakata da fina-finai da CMG ta gabatar kan wannan jigo, ciki hadda fim din da ya bayyana labarai na "Muna bin babbar hanya", da fim din "A wannan lokaci: babban bikin faretin soja na 2019" da aka gabatar bisa fasahar 4K. Ban da wannan kuma, mun samu sakonnin fatan alheri daga abokanmu a kasashe daban-daban. Masanin kasar Italiya mai nazarin harkokin kasar Sin Francesco Maringio ya bayyana a cikin sakonsa na E-mail cewa, "Ina jinjinawa ci gaba mai armashi da Sin ta samu a cikin shekaru 70 da suka gabata, a ganina, ya kamata Sinawa su yi alfahari da wadannan ci gaba."

A cikin shekarar da ta gabata, mun yi kokarin gabatar da labarai kan dukkan wani ci gaban da Sin ta samu dake jawo hankalin mutane, don gabatarwa duk duniya wata kasar Sin mai cikakken gaskiya daga fannoni daban-daban. Har mun yi amfani da wasu fasahohin zamani kamar su 5G, 4K ko 8K da kwaikwayon tunanin dan-Adam (AI) da dai sauransu, inda muka cimma nasarar ba da labarai kan dandalin koli na hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar "Ziri daya da hanya daya", da babban taron karawa juna sani kan wayewar kan Asiya, da kuma bikin murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin Macao karkashin mulkin gwamnatin kasar Sin da sauransu. Kazalika, fina-finai da muka gabatar mai suna "Bayanai na tarihi da Xi Jinping ya fi so" da kuma "Idan abubuwan tarihi masu daraja na kasar Sin sun iya yin magana" da sauransu, wadanda suka samar da wata sabuwar hanya ga abokan ketare domin kara sani da fahimtar al'adu masu dogon tarihi da muradun kasar Sin a sabon zamani, ban da wannan kuma, abokanmu na jin dadin ayyukan da muka gudanar, abin da ya sa suna kaunar kasar Sin kwarai, ciki hadda "Tafiya tare da kasar Sin", da "Kara sada zumunta tsakanin Sin da Rasha cikin farin ciki" da kuma yadda masu gabatar da labarai a intanet ta harsuna daban-daban ke samun karbuwa sosai da dai sauransu.

Bai kai shekaru biyu da kafa CMG ba, amma mun fahimci cewa, a cikin sabon zamani na Intanet, idan babu ci gaba mai sauri, za a samu koma baya. Muna nacewa ga bukatar shugaba Xi Jinping wato "Nacewa ga gaskiya da yin kikire-kirkire don kafa da yin amfani da Intenat da sabon dandali yadda ya kamata", da kuma tsayawa tsayin daka kan kara saurin bunkasuwa don zama wata kafa dake sahun gaba a duniya ta hanyar yin kirkike-kirkire. A cikin wannan shekara, mun kafa muhimmin dakin hada fina-finai da cibiyar gwaji mai amfani da fasahohin zamani, wadda ta kasance irinta daya kacal a kasar Sin, da kuma yin iyakacin kokarin kafa dandali na zamani mai fasahar 5G na "Bidiyon CMG", kana domin kyautata aikinmu, mun gabatar da shirye-shirye masu inganci sama da 200, ta yadda masu kallo da sauraro za su shakata da shirye-shiryenmu.

Muna bin ka'idar samar da labaran duniya bisa daidaito da adalci a dukkan fannoni. Muna kokarin kan bude kofa, hadin kai da kara musanyar ra'ayoyi da abokanmu na gida da ketare a wannan fanni. A cikin wannan shekara, mun tattauna da abokanmu na kafofin yada labarai fiye da 150 a duniya, ciki hadda AP, Reuters, AFP, BBC da dai sauransu, inda muka kai ga cimma matsaya da ma habaka zumunci a duniya.

Duk da wadannan ci gaban da muka samu a wannan fanni, mun ga yadda idanun wasu kafofin yada labarai na kasashen yamma sun rufe a kan wasu muhimman abubuwa da suka shafi kasar Sin, inda suka yada labarai bisa jita-jita, wasu labaran ma kamar almara. A ganinmu, gaskiya abu mafi muhimmanci na labarai, idan an ba da labarai bisa tunani ko mai da labarai a matsayin almara, hakan zai zubar da mutuncin ko wace kafar yada labarai. Wannan gargadi ne ga shugabannin kafofin yada labarai a duniya gaba daya.

Wani marubuci na karni na 18 na kasar Birtaniya William Hazlitt na da wani karin magana dake bayyana cewa: "Rashin fahimta shi ne tushen jahilci". Hakika, kokarin neman gaskiya da kawar da bambancin ra'ayi suna da ma'ana sosai. CMG zai ci gaba da yada labarai bisa gaskiya da daidaito da adalci.

Marubucin wakoki a zamanin daular Tang na kasar Sin Zhang Jiuling ya nuna cewa: "Abokan juna ba su tsoron nisa, duk da nisa dake tsakaninsu, suna tunanin juna". Muna rayuwa a cikin wannan duniya, mu abokan juna ne. Lokacin da na kai ziyara Brazil da Argentina, na yi farin ciki sosai da ganin furen Jacaranda da furen Bougainville, na kuma saurari kukan wani tsuntsu mai kama da na kyanwa, wadanda na saba gani da sauraro a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, ban da wannan kuma a Italiya da Spaniya, na dandana barasar shinkafa wadda ta yi kama da ta garina dake lardin Zhejiang, duniya tamkar kauye ne gaba daya ga bil Adama. A cikin wannan kauye, babu bambancin ra'ayi, a maimakon haka sai kara tuntuba da musanya da haduwa. A ganina, yayin mu'ammalar kafofin yada labarai, ya kamata a kawar da bambancin ra'ayi, ta yadda mutane daga wurare daban-daban za su sada zumunta su zama aminai.

Dadin dadawa, shekarar 2020 wata muhimmiyar shekara ce ta raya al'ummar Sinawa mai matsakacin wadata, kuma za a cimma nasarar kawar da kangin talauci tsakanin mutanen da yawansu ya kai bilyan 1.4, wanda ba a taba ganin iri wannan nasara ba a tarihin bil Adama. CMG zai yi iyakacin kokarinsa don yada labaran gida da na waje, da kuma ba da gudunmawa wajen raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.

Kauna ta mamaye ko ina a shekarar 2020

Fatan alheri ga kasar Sin, fatan alheri ga duniya, kuma ina muku fatan alheri.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China