Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 4 sun mutu sanadiyyar hadarin mota a arewacin Najeriya
2019-12-18 12:00:12        cri

An gano gawawwakin mutane 4 a ranar Talata a wajen da aka samu hadarin mota a jihar Kwara dake shiyyar arewa ta tsakiyar Najeriya, wani jami'in dan sanda mai tsaron hanya ya tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sanda ya ce, hadarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da wata motar fasinjoji ta yi taho mu gama da babbar mota a babban titin mota na Omu-Aran-Oke-Onigbin a jihar Kwara.

Hadarin ya yi sanadiyyar haddasa cunkoson ababen hawa na tsawon sa'o'i a safiyar ranar Talata a babban titin mai fama da yawan zirga zirga ababen hawa.

A cewar Festus Adetunji, shugaban jami'an 'yan sandan kiyaye hadurra na jihar Kwara, babbar motar ta tura motar fasinjojin gefen hanya.

Adetunji ya dora alhakin faruwar hadarin kan gudun da ya wuce kima, da tukin ganganci, kana ya gargadi direbobin mota da su guji karya dokokin tuki.

Ya ce kusan kashi 70 bisa 100 na hadduran mota da ake samu a titinan motan Najeriya mutane ne ke haddasu ta hanyoyin mummunan gudu da tukin ganganci.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China