Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin Sin ta yi kira ga Amurka da ta kauracewa aiwatar da matakai marasa kyau
2019-12-27 09:33:09        cri

Kakakin rundunar sojojin kasar Sin Wu Qian, ya yi kira ga kasar Amurka, da ta kauracewa aiwatar da wasu miyagun matakai masu nasaba da Sin, karkashin tanajin dokar kasafin kudinta na ayyukan soji na shekarar 2020.

Wu Qian, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da tanajin dokar tsaron kasa da Amurka ta amincewa, mai kunshe da wasu sassa da ka iya zama tsoma baki cikin harkokin yankin Taiwan, da Hong Kong da Xinjiang. Jami'in ya ce rundunar sojin Sin na matukar adawa da wannan mataki.

Ya ce matakan tsoma baki cikin harkokin Sin, na nuni ga rungumar tunanin cacar baka, matakin da ka iya dagula yanayin takara tsakanin Sin da Amurka, da ma yayata zargin nan da ake yi na "kasancewar rundunar Sin barazana ga wasu sassa.".

Kaza lika aiwatar da wannan doka tamkar yunkuri ne na gurgunta alakar Sin da Amurka a fannin hadin gwiwar ayyukan soji, mataki ne kuma da zai rushe amincewa da juna da hadin kan sassan.

Wu Qian, ya kuma yi watsi da zargin nan da ake yi, na "kasancewar rundunar Sin barazana ga wasu sassa." Sabanin yadda wasu manyan jami'an rundunar sojin Amurka ke yayata hakan.

Ya ce irin wannan zargi tamkar nuna gazawar ita kan ta Amurka ne, duba da cewa bai ma kamata Amurkan ta zargi wata kasa a wannan fanni ba, duba da irin makuden kudade da take kashewa a bangaren ayyukan soji, da ma zargin da ake yi mata a fannin leken asiri ta yanar gizo, da kuma wasu batutuwa masu nasaba da hakan.

Daga nan sai ya yi kira ga Amurka, da ta sauya matsayinta game da batutuwa da suka shafi kasar Sin, da harkokin tsaro, da na duniya baki daya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China