Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Habasha za su bunkasa hadin gwiwa a fannin gine-gine
2019-12-26 11:26:22        cri
Ma'aikatar raya birane da gine-gine ta kasar Habasha ko MoUDC a takaice, ta ce mahukuntan kasar, da wasu kamfanonin kasar Sin, sun amince da aiwatar da hadin gwiwa, wajen bunkasa sashen gine-ginen kasar.

Wata sanarwar da MoUDC din ta fitar, ta ce an cimma yarjejeniyar hadin gwiwar ne, yayin da ministar raya birane da gine-gine ta kasar Habasha Aysha Mohammed, ta ziyarci wasu kamfanonin gine-gine na kasar Sin.

Sanarwar ta rawaito ministar na cewa, Habasha ta tsara muhimman kudurorin bunkasa harkar gine-gine a kasar na shekaru 10, kuma kamfanonin gine-gine na Sin, na da rawar takawa wajen tabbatar da cimma nasarar wadannan kudurori.

Aysha Mohammed ta kara da cewa, Habasha na fatan samun tallafi daga Sin a fannin tsara gidajen kwana, ga miliyoyin al'ummarta wadanda suke fama da karancin muhalli mai nagarta.

Kaza lika Habasha, wadda ke samun tagomashin tattalin arziki cikin shekaru 15 kawo yau, sakamakon bunkasar sashen gine-gine, a yanzu tana aiwatar da gine-gine gidajen kwana masu yawa, a wani mataki na cika alkawuranta na raya tattalin arziki, da inganta rayuwar jama'a, bukatun da ko shakka babu, na da nasaba da karuwar al'ummun ta mazauna birane. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China