Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta jinjinawa sauye-sauyen da Habasha ta gudanar
2019-11-13 10:34:46        cri
Mambobin hukumar bunkasa zaman lafiya ta MDD, sun jinjinawa sauye sauye da mahukuntan kasar Habasha suka aiwatar a fannin jagoranci, suna masu bayyana matakin a matsayin abun da zai haifarwa kasar da mai ido, duba da cewa, sauye-sauyen sun dace da manufofin ciyar da kasar gaba, da kuma wanzar da zaman lafiya.

Mambobin hukumar sun yi wannan tsokaci ne yayin ganawarsu da shugabar kasar Habasha Sahle-Work Zewde a ranar Talata.

Wata sanarwa da ofishin shugabar kasar ya fitar, ta rawaito shugaba Zewde na bayyanawa jami'an, muhimmancin amfani da kwarewa, da dorawa daga inda aka tsaya, yayin aiwatar da manufofin wanzar da zaman lafiya. (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China