Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha na neman hadin gwiwa da Sin a bangaren makamashi
2019-10-23 09:31:50        cri
Ministan kula da albarkatun ruwa da noman rani da makamashi na kasar Habasha, Firehiwot Woldehana, ya ce kasar na neman inganta samar da makamashi, a don haka take fatan kara hadin gwiwa da aiki da kamfanonin kasar Sin da za su iya lalubo damarmakin dake akwai, a kasar ta gabashin Afrika.

Da yake jawabi ga taron hadin gwiwa kan makamashi tsakanin Sin da Afrika, jiya a birnin Addis Ababa, ministan ya ce gwamnati na aiki tukuru don ganin ta inganta yanayin da ake ciki a kasar ta fuskar samar da makamashin lantarki, wanda ke kaso kan 44 cikin dari a yanzu, inda aka hada wanda ke hade da turakun lantarki da wanda ba ya hade da shi.

Ya kuma bayyana cewa, burin kasar shi ne samar da lantarki ga kowa cikin shekaru 6 masu zuwa, yana mai cewa bangaren na kunshe da damarmaki ga baki masu zuba jari, ciki har da kamfanonin kasar Sin.

Chen Chao, wakilin kamfanin SGCC CET na kasar Sin a wajen taron, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, taron ya samar da dandali mai kyau na musayar bayanai da dabaru a bangaren makamashi. Kamfanin SGCC CET wani bangare ne na kamfanin samar da lantarki na kasar Sin.

Chen Chao ya kara da cewa, Sinawa za su kara karfafa hulda da Afrika, musammam ma Habasha, a bangaren makamashi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China