Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoton MDD ya yabawa ci gaban da Habasha ta samu wajen inganta rayuwar yara da mata
2019-10-22 09:31:49        cri
Wani rahoto da aka wallafa jiya Litinin, ya ce Habasha ta samu nasara wajen inganta rayuwar yara da mata cikin shekaru 5 da suka gabata, inda alkaluma a fannonin lafiya da abinci mai gina jiki da ilimi da kare yara suka nuna an samu ci gaba.

Rahoton nazarin rayuwar yara da mata a Habasha na 2019, wanda asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF da gwamnatin kasar suka wallafa, ya tabbatar da ci gaban da aka samu a baya-bayan nan kan harkokin yara da mata a Habasha, yayin da yake jaddada cewa, kasar na ci gaba da fuskantar kalubale wajen karfafawa al'ummar kasar.

A cewar Adele Khodr, wakiliyar UNICEF a Habasha, rahoton ya nuna cewa, idan gwamnati ta himmantu wajen kyautata rayuwar yara, kamar yadda Habasha ta yi cikin shekaru 20 da suka gabata, rayuwar yara za ta ingantu, sannan za su samu damar yin duk abun da suke da muradi.

Sai dai, kamar yadda rahoton ya nuna, akwai sauran aiki a gaba, na kawo karshen mace macen jarirai, da kara fadada alluran rigakafi da rage matsananciyar tamowa da kawo karshen auren wuri da sanya kowane yaro a makaranta da fadada samar da tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli da kuma rage fatara a tsakanin yara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China