Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IOM: Yan kasar Habasha 113 sun koma gida daga Djibouti
2019-11-24 16:19:28        cri
Hukumar kula da 'yan ci rani ta kasa da kasa, (IOM), ta sanar a ranar Asabar cewa ta mayar da 'yan kasar Habasha 113 zuwa kasarsu daga Djibouti.

A sanarwa da aka rabawa manema labaru, IOM ta ce, 'yan ci ranin na kasar Habasha dukkansu maza ne, an tanadar musu da kudaden guzuri da wuraren kwana a cibiyar kula da 'yan ci rani ta MDD dake Addis Ababa bayan da suka isa kasar da yammacin ranar Juma'a.

An yi kiyasin cewa dubban 'yan kasar Habasha ne suke fakewa a kasar Djibouti a duk shekara, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasashen larabawa.

Mafi yawan 'yan ci ranin kasar ta Habasha suna gararamba ne a kasar Djibouti wadanda masu safarar bil adama ke kwace musu dukkan kudade da kayayyakin da suka mallaka inda suke barinsu cikin matsanancin talauci a kasar ta gabashin Afrika.

Da dama daga cikin 'yan ci ranin na Habasha ana kama su tare da tuhumarsu da laifukan shiga kasar ta haramtattun hanyoyin suna shafe watanni ko kuma shekaru a gidajen yarin kasar Djibouti.

A duk shekara, hukumar IOM tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar Habasha da hukumomin kasar Djiboutian suna tisa keyar daruruwan 'yan ci ranin Habasha dake gararamba. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China