![]() |
|
2019-09-01 16:25:55 cri |
Bakin hauren, wadanda galibinsu 'yan kasashen yankin hamadar saharar Afrika ne, sun yi amfani da kananan kwale kwale wadanda suke da matukar hadari yayin tsallakawa tekun na Meditereniya, a cewar wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na MAP ya wallafa.
Sanarwar ta kara da cewa, bakin hauren, sun hada da mata da kananan yara da dama, an ba su kulawar gaggawa ta farko a wata cibiyar da sojojin ruwan kasar Morocco suka kafa, kafin daga bisani a kwashe su zuwa tashar ruwan tekun Meditereniya.
Morocco ta kasance tamkar wata hanya ce inda bakin haure daga kasashen Afrika ke amfani da ita wajen tsallakawa zuwa kasashen Turai domin samun ingantacciyar rayuwa.
Morocco ta tusa keyar bakin haure kimanin 57,000 tun daga farkon shekarar 2019, wadanda ke kokarin tsallakawa zuwa Turai ta barauniyar hanya, kakakin gwamnatin kasar Mustapha El Khalfi shi ne ya bayyana hakan. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China