Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kada a bar raayin ba da kariya kan ciniki ya hana yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa
2019-06-27 11:15:19        cri

Kwanan baya, Nasser Bouchiba, shugaban hadaddiyar kungiyar rayawa da yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kasar Morocco ya bayyana wa wakilinmu cewa, kara yin tattaunawa a kokarin cimma daidaito, hanya ce mafi dacewa ta kawar da sabanin tattalin arziki da ciniki, da tabbatar da daidaiton tattalin arzikin duniya. Ya ce bai kamata a bar ra'ayin ba da kariya kan harkokin cinikayya ya hana yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ba.

A daidai lokacin da ake kara samun rashin tabbaci a duk duniya baki daya, za a gudanar da taron koli na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki 20 wato G20 a birnin Osaka na kasar Japan gobe Jumma'a 28 ga wata. Haka kuma, takaddamar cinikayya tsakanin kasashen Sin da Amurka ta haifar da illa kan makomar tattalin arzikin duniya, lamarin da ya ja hankalin sassa daban daban na Afirka.

Yayin da yake zantawa da wakilinmu, Nasser Bouchiba ya kara da cewa, yanzu yawancin mutane sun amince da kasancewar matakai daban daban a duniya. Duk wata kasa da ta dauki tsattsauran matakan ba da kariya kan harkokin ciniki, kasa ce da ba ta sauke nauyinta ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China