Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Ghana ya kaddamar da rukunin masana'antun da kasar Sin ta gina a Tema
2019-12-20 12:45:15        cri

Shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo na kasar Ghana, ya kaddamar da rukunin masana'antun da kasar Sin ta gina a Tema dake kusa da Accra, babban birnin kasar. Shugaban ya bayyana aikin a matsayin misali na ci gaban alakar tattalin arziki tsakanin Sin da kasar Ghana, baya ga taimakawa kasar wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare.

A nasa jawabin, jakadan kasar Sin dake Ghana, Wang Shiting, ya bayyana cewa, kafa irin wadannan rukunin masana'antu, ya dace da manufar kasar Ghana ta "Gunduma daya kamfani daya". Ya kuma bayyana kudurin kamfanonin kasar Sin na zuba jari a Ghana don amfanin bangarorin biyu.

Ana saran rukunin masana'antun da rukunin kamfanin Green house International Development na kasar Sin ya gina, zai hada kamfanonin 100 wajen guda da samar da guraben ayyukan yi kimanin 300,000.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China