Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani babban bankin Afrika ya bude kofa ga kamfanonin Sin dake Ghana
2019-06-08 16:24:13        cri

Bankin Access Bank, daya daga cikin manyan bankunan dake sahun gaba a Afrika, ya sanar a ranar Juma'a cewa ya bude kofofinsa na tallafawa kamfanonin 'yan kasuwar kasar Sin dake gudanar harkokinsu a kasar Ghana.

Da yake jawabi a lokacin taron dandalin 'yan kasuwar kasar Sin wanda bankin ya shirya, Olumide Olatunji, manajan daraktan bankin Access na Ghana, ya ce abin alfahari ne kulla huldar ciniki da kamfanonin kasar Sin.

Olumide ya kara da cewa, "Bankin Access ya kafa cikakken tsarin ciniki ga kamfanonin kasuwancin kasar Sin dake Ghana. Wannan tsarin ya samu goyon bayan wakilan ofisoshinmu dake kasar Sin wadanda suka taimaka mana wajen shirya harkokin cinikayya da kuma samar da kudaden tafiyar da harkokin ciniki ga abokan huldarmu da muke mu'amala tare."

Cinikayya tsakanin kasar Sin da Ghana ya karu daga dala biliyan 2.1 a shekarar 2010, zuwa dala biliyan 6.6 a shekarar 2018.

Yin Jun, babban sakataren majalisar 'yan kasuwar kasar Sin dake Ghana, ya bayyana kyakkyawar fata game da tallafin da bankin ya baiwa 'yan kasuwar na kasar Sin, inda ya ce matakin zai kara bunkasa harkokin kasuwanci a kasar kana zai taimaka wajen bunkasuwar tattalin arzikin kasar Ghana.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China