Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin StarTimes na kasar Sin ya kaddamar da wani shirin inganta fasahar matasa masu basirar kwallon kafa a Ghana
2019-11-15 10:42:31        cri

Kamfanin StarTimes na kasar Sin, mai watsa shirye-shiryen talabijin, ya gabatar da wani shirin dake da nufin inganta fasahar matasa masu basirar kwallon kafa da masu ba da horo a Ghana.

Shirin wanda aka yi wa lakabi da Bundesliga Football School wato BFS a takaice, na hadin gwiwa ne tsakanin Kamfanin StarTimes da Kungiyar kwallon kafa ta Bundesliga ta kasar Jamus.

A cewar sanarwar da kamfanin StarTimes ya fitar, BFS sabon shirin hadin gwiwa ne dake da nufin raya da inganta kwarewar matasa masu basira a fadin duniya.

Sanarwar ta kara da cewa, shirin zai kunshi kungiyoyin kwallon kafa da gasanninsu da manyan kungiyoyin kwallo domin karfafa gwiwar matasan daga tushe.

Cikin kwas din mako guda da za a yi watan Disamba, samari da 'yan mata dake tsakanin shekaru 13 zuwa 17, za su samu jerin horo da tarukan karawa juna sani.

Matasan za su samu horon ne daga kwararru da masu ba da horo dake da lasisi daga cibiyoyin horar da matasa na kungiyoyin Bundesliga da taimakon wasu masu bada horo na kasar da aka zabo. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China