Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana sun yaba taimakon kasar Sin wajen bunkasa bangaren samar da iccen Gora a gabashin Afirka
2019-10-14 20:05:26        cri

Manajan na kungiyar shirin kasa da kasa kan raya iccen Gora da Rattan (INBAR) mai kula da ofishin gabashin Afirka Jayaraman Durai, ya bayyana cewa, kasar Sin tana taimakawa wajen bunkasa masana'antar raya iccen Gora a kasashen gabashin Afirka.

Masanin ya bayyana hakan ne, yayin da wata zantawa ta musamman da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yana mai cewa, yadda kasar Sin take taimakawa da fasahohinta, hakan ya taimaka wajen raya masana'antar iccen Gora a kasashen Habasha, da Uganda da Kenya.

Kungiyar INBAR mai mambobin kasashe 44, tana mayar da hankali ne wajen raya masana'antun iccen Gora da rattan. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China