Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsohon shugaban Babban Bankin Nijeriya ya yi gargadin cewa kasar na gab da fuskantar karayar arziki
2019-06-26 11:13:20        cri
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Muhammad Lamido Sanusi, ya yi gargadin cewa, kasar na gab da fuskantar karayar arziki, biyo bayan daukar wasu dabarun da ba su dace ba, kamar na tallafin albarkatun man fetur da harajin lantarki.

Da yake bayani a jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya, Muhammad Lamido Sanusi, ya shawarci gwamnatin shugaban kasar Muhammadu Buhari, ta soke tallafin man fetur da harajin lantarki idan har tana son daidaita tattalin arzikin kasar.

Ya ce abun da ya fi barazana fiye da tallafin rarar man fetur shi ne, sadaukar da ilimi da kiwon lafiya da ababen more rayuwa don samun man fetur mai rahusa.

Wannan na zuwa ne kasa da watanni biyu, bayan tsohon shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Abdulazizi Yari, ya yi gargadin cewa, akwai yuwuwar kasar ta kara fadawa cikin matsalar tattalin arziki.

Abdulaziz Yari ya gargadi sababbin Gwamnonin, su shirya tunkarar wani zagaye na tabarbarewar tattalin arziki a tsakiyar shekarar 2020 zuwa rubu'i na 3 na shekarar 2021.

Nijeriya ta shiga matsalar tattalin arziki karon farko cikin shekaru sama da 20 ne a watan Augustan 2016, kamar yadda wasu alkaluma suka nuna cewa, tattalin arzikin kasar ya ragu cikin rubu'i biyu a jere. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China