Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bankin duniya: Tattalin arzikin yankin Afrika dake kudu da Sahara zai karu da kashi 2.6% a bana
2019-10-10 09:18:01        cri
Wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar a ranar Laraba ya nuna cewa, an yi hasashen tattalin arzikin kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara zai karu daga kashi 2.5% a shekarar 2018, zuwa kashi 2.6% a shekarar 2019.

A rahoton bankin game da tattalin arzikin Afrika karo na 20, ya nuna cewa, matsayin bunkasuwar tattalin arzikin shiyyar a shekarar 2019 bai taka wata rawar a zo a gani ba sakamakon matsalolin rashin tabbas game da makomar tattalin arzikin duniya, da kuma tafiyar hawainiyar da ake samu wajen aiwatar da muhimman gyare-gyaren da za su bunkasa tattalin arzikin shiyyar.

Muhimmin taken wallafar ta mayar da hankali ne kan irin gibin da ya kamata a cike, musamman game da batun da ya shafi mata da mutanen da suka fi fuskantar kangin fatara.

Binciken ya bayyana cewa, shirin bunkasa sana'o'in dogaro da kai na mata wani muhimmin al'amari ne ga ci gaban dukkan al'ummar kasashen Afrika. Yankin Afrika dake kudu da Sahara shi ne kadai yanki a fadin duniya wanda zai iya karfafawa mata gwiwa wajen samun sana'o'in dogaro da kai sama da takwarorinsu maza, a cewar rahoton.

Bankin na duniya ya ce, matan Afrika su ne ke bayar da kaso mafi girma wajen gudanar da ayyukan kwadago a fannin aikin gona a duk fadin nahiyar.

To sai dai kuma, batun yawan nasarorin da ake tsammanin samu ta fuskar yawaitar shigar mata aikin kwadagon wajen habaka aikin gona yana ci gaba da gamuwa da cikas sakamakon gibin dake tsakanin mata da maza a wannan fanni. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China