2019-12-19 10:51:15 cri |
A jawabinta yayin taron, Lu Xi, mai jagoran tawagar wakilan kasar Sin, ta bayyana ra'ayin kasar Sin kan wannan batu. Ta nuna yabo matuka kan babbar gudummawar da yarjejeniyar da aka kulla ta samar wa kasa da kasa wajen karfafa hadin gwiwa kan aikin yaki da cin hanci da karbar rashawa, ta kuma yi bayani kan yadda kasar Sin ta inganta hadin gwiwar dake tsakaninta da gamayyar kasa da kasa, da fasahohin kasar game da dawo da dukiyoyin da aka sata, sa'an nan, ta yi kira ga kasashen da aka boye dukiyoyin masu cin hanci da rashawa, da su daidaita ra'ayinsu na siyasa, su taimaka wajen dawo da wadannan kudade yadda ya kamata.
Bugu da kari, ta ce, kasar Sin tana goyon bayan gudanarwar babban taron musamman na MDD kan batun yaki da cin hanci da karbar rashawa a shekarar 2021, ta jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su martaba yarjejeniyar yaki da cin hanci da karbar rashawa yadda ya kamata, su kuma tsaya tsayin daka kan ka'idojin adalci da cimma moriyar juna, mutunta bambancin dake tsakanin bangarori daban daban, aiwatar da ayyukan da abin ya shafa cikin sauri, da hukunta duk wanda ke aiwatar da cin hanci da karbar rashawa, ta yadda za a kafa wani tsari mai inganci, wanda ba zai ba da dama ga wadanda suke son cin hanci da karbar rashawa ko kadan ba. Haka kuma, ya kamata mu karfafa hadin gwiwarmu kan wannan aiki, ba tare da gindaya wani sharadi ba, domin hana a adana kudaden masu cin hanci da karbar rashawa. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China