Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Al'ummomin yankin Macao dake janyo hankalin shugaba Xi
2019-12-18 15:07:57        cri

Ranar 20 ga watan Disamba, shekaru 20 ke nan da dawowar yankin Macao kasar Sin. A wannan shekara da ake murna, wasu yara da tsofaffin yankin, sun sami amsar wasikun da suka rubutawa shugaba Xi Jinping. Cikin wasikunsa, shugaba Xi ya kula sosai game da abubuwan da suka shafi al'ummomin yankin. A duk lokacin da ya kai ziyarar aiki yankin, Xi Jinping ya kan ziyarci wuraren da jama'a ke zaune, ya yi hira da dalibai game da harkokinsu na karatunsu, ya kuma yi hira da ma'aikata da shugabannin kamfanonin yanki kan harkokin zaman rayuwar tasu, lamarin da ya burge al'ummomin yankin matuka.

"Ko ka san cewa, Macao ba shi ne ainihin sunana ba, mun dade ba mu sadu ba, mahaifiyata…"

A shekarar 1999, aka fitar da "Wakar yara guda 7 na kasar Sin", wadda ta burge dukkanin al'ummomin kasar Sin sosai, an kuma zabi wannan waka a matsayin wakar maraba da dawowar yankin Macao karkashin ikon kasar Sin. A bana kuma, wato bayan shekaru 20 da suka gabata, daliban makarantar firamare ta Gwani sun aikawa shugaba Xi Jinping wasiku, inda suka bayyana yadda suka fahimci kalmar "Kasar haihuwata", cikin wasikun da shugaba Xi ya amsa, ya ce, "Yadda yara suka nuna bege kan mahaifiya cikin wakar 'yara guda 7 na kasar Sin', ta burge mu sosai. Bayan dawo da yankin Macao karkashin ikon kasar Sin, cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, yankin ya sami babbar bunkasuwa a fannoni daban daban, zaman rayuwar al'ummomin yankin yana ci gaba da samun kyautatuwa. Kasar Sin tana goyon bayan yankin Macao, kun san wannan tun kuna kananan yara, lalle na yi farin ciki sosai".

Amsar wasikun da shugaba Xi ya rubutawa daliban yankin Macao ta nuna yadda shugaba Xi ya kula da zaman rayuwar al'ummomin yankin. cikin shekaru 10 da suka gabata, Xi Jinping ya ziyarci yankin Macao sau biyu, yana kuma mai da hankali kwarai da gaske kan ko al'ummomin yankin suna jin dadin zama, da kuma ko yankin zai iya samun dauwamammen ci gaba a fannin tattalin arziki da zaman takewar al'umma.

"Gaishe ka, dukkan wadannan 'ya'yan ka ne?"

"E, ina da 'ya'ya guda uku."

"Da kyau, kamar furannin zinariya guda uku…"

A shekarar 2014, wato shekaru 15 da dawo da yankin Macao karkashin ikon kasar Sin, Xi Jinping ya kai ziyara a gidajen al'umma na Shek Pai Wan, wato gidajen al'umma mafi girma a yankin, domin ya ziyarci gidajen fararen hula, da kuma ganin yadda suke zaman rayuwa. A lokacin ya san, iyalan Tan Yu'e sun kaura zuwa sabon gida sama da tsawon watanni 8, Xi Jinping ya ce, "Da gani suna jin dadin zaman rayuwarsu, dukkan iyalai na waje guda, za su sami makoma mai kyau, tabbas makomarsu a nan gaba za ta yi kyau."

A watan Oktoba na bana, an bude babbar gadar Hong Kong-Zhuhai-Macao a hukumance, shugaba Xi ya halarci bikin bude babbar gadar, inda ya kuma bayyana cewa, "Kaddamar da babbar gadar tana da muhimmiyar ma'ana, gadar ta kasance babban aiki na kasar Sin, kuma babban aiki a fadin duniya. Haka kuma, gadar ta taimaka wajen hada biranen babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao. Sa'an nan kuma, an gina wannan gada bisa manufar 'kasa daya amma tsarin mulki biyu', shi ya sa, gina babbar gadar yana da muhimmiyar ma'ana. Yau, mun cimma burinmu."

An kafa babbar cibiyar taimakawa tsofaffi ta Yi Jun ta yankin Macao a shekarar 2007, wadda take mai da hankali kan kula da tsofaffi. A watan Janairu na shekarar 2009, mataimakin shugaban kasar Sin na wancan, Xi Jinping ya kai ziyara a wannan cibiya. Sa'an nan, a bikin tsakiyar kaka na bana, tsofaffi masu aikin sa kai dake cibiyar guda 30 sun aikawa shugaba Xi Jinping wasika, inda suka bayyana babban ci gaba da yankin Macao ya samu bayan da aka dawo da yankin karkashin ikon kasar Sin, da kuma alfaharin da suka ji saboda zama 'yan kasar Sin. Sa'an nan, kafin zuwan bikin tsofaffi, shugaba Xi ya amsa musu cewa, yana fatan suna zaune lafiya da kuma jin dadi.

Malama Chen Yulian mai shekaru 75 ta taba yin hira da dinki kayan sana'ar hannu tare da shugaba Xi a shekarar 2009, da take tunanin lokacin, ta ce, "A shekarar 2009, shugaba ya taba gaya min cewa, ya kamata mu kara yin musaya, shi ya sa, na aika masa wasika domin na gaisa da shi, na kuma gaya masa cewa, an dawo da yankin Macao karkashin ikon kasar Sin yau shekaru 20, yanzu zaman rayuwarmu ya samu kyautatuwa kwarai da gaske! Ban yi zaton cewa, shugaba zai amsa min da sauri haka, na yi farin ciki, na kuma ji dadi a zuciyata sosai."

Cikin wasikun da shugaba Xi ya aikawa tsofaffin, ya ce, sun ga irin babban ci gaba da kasar Sin ta samu, sun kuma ga yadda aka cimma nasarar aiwatar da tsarin "kasa daya amma tsarin mulki biyu" a yankin Macao. Bugu da kari, shugaba Xi ya ce, yana fatan wadannan tsofaffi za su ci gaba da ba da gudummawa, su kuma fadawa matasan yankin Macao labarai game da yadda yankin ya sha bamban bayan da aka dawo da shi karkashin ikon kasar Sin. Da kuma sa kaimi ga matasan yankin don su ba da gudummawa wajen gina babban yankin Guangdong-Hong Kong-Macao, ta yadda yankin Macao zai samu wata makoma mai haske. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China