Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yankin Macao na Sin ya ci gaba da habaka mu'amalarsa da kasashen duniya
2019-12-06 14:56:51        cri

Bana, shekaru 20 ke nan da yankin Macao ya dawo hannun kasar Sin, kana shekaru 20 da kafa hukumar wakilan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin Macao. Cikin shekaru 20 da suka gabata, hukumar wakilan ma'aikatar harkokin wajen Sin dake yankin, da yankin Macao sun sami ci gaba cikin hadin gwiwa, kuma sun ba da gudummawa wajen aiwatar da tsarin "kasa daya tsarin mulki biyu" a yankin yadda ya kamata, da kuma cimma nasarar habaka harkokin diflomasiyyar yankin Macao na Sin.

A ranar 5 ga wata, hukumar wakilan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin Macao ta shirya liyafar murnar cika shekaru 20 da kafuwa. Mataimakin shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Edmund Ho Hau-wah, da kantoman yankin Macao Fernando Chui Sai On, da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng, da wakiliyar hukumar wakilan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin Macao Shen Beili sun halarci wannan liyafa.

A shekarar 1999 ne, aka kafa yankin musamman na Macao a hukumance, wanda ya zama muhimmiyar alamar dunkulewar kasar Sin, da farfadowar al'ummar kasa, kana, al'ummomin yankin Macao sun sami cikkaken 'yancin tafiyar da harkokin yankinsu. Daga wannan lokaci ne, yankin Macao mai dogon tarihi ta fuskar mu'amalar al'adu tsakanin gabashi da yammacin duniya, ya fara samun sabuwar bunkasuwa. Kana, a matsayinsa na muhimmiyar gadar Sin da ta hade yammaci da gabashin duniya, birnin Macao yana janyo hankulan kasa da kasa.

Kantoman yankin Macao Fernando Chui Sai On ya bayyana cewa, tun bayan da aka hade yankin Macao kasar Sin, yankin ya sami gagarumin ci gaba a ayyukan dake shafar kasashen waje, sabo da tsarin musamman na "kasa daya tsarin mulki biyu", da kuma kariyar da "kundin tsarin mulkin kasa" da "babbar dokar Macao" suka baiwa yankin. Ya ce, "Bisa babbar gudummawar da gwamnatin tsakiya da hukumar wakilan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin suka baiwa yankin Macao, yankin ya shiga karin kungiyoyin kasa da kasa, da kulla yarjejeniyoyin kasa da kasa da dama. Kana, adadin kasashe da yankuna da suke baiwa al'ummomin yankin Macao takardun biza kyauta yana karuwa. Bugu da kari, a matsayinsa na yankin Macao na kasar Sin, yankin ya kulla yarjejeniyoyin kasa da kasa da dama, wadanda suka shafi fannonin tattalin arziki, da ciniki, da hada-hadar kudi, da jiragen saman fasinja da dai sauransu. Haka kuma, hukumar wakilan ma'aikatar harkokin wajen Sin dake yankin Macao ta taimakawa yankin wajen gudanar da tarukan kungiyoyin kasa da kasa da dama."

Cikin shekaru 20 da suka gabata, tattalin arzikin yankin Macao ya bunkasa matuka, kuma alkaluma kan jin dadin rayuwar jama'ar yankin yana karuwa. A sa'I daya kuma, yankin yana ci gaba da habaka mu'amalar dake tsakaninta da kasashen ketare, har ma ya cimma nasarori da dama ta fuskar kafa cibiyar yawon shakatawar kasa da kasa, da dandalin hadin gwiwar kasuwanci tsakanin Sin da kasashe masu amfani da harshen Portugal da dai sauransu. Kana, alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a bara, adadin wadanda suka ziyarci yankin Macao ya kai miliyan 36.

Haka zakila, hukumar wakilan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin Macao ta ba da gudummawa matuka kan raya harkokin kasa da kasa a yankin Macao. Wakiliyar hukumar Shen Beili ta bayyana cewa, hukumar ta taimakawa yankin Macao wajen kafa "cibiya daya, dandali daya da sansani daya", domin karfafa alakar bangarori daban daban dake cikin hadin gwiwar shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma taimaka wa yankin Macao wajen kafa wani dandalin yin hadin gwiwa da babban yankin kasar Sin, da ma kasashen dake kewaye da shi, da kuma habaka mu'amalar yankin Macao da birane na ketare, da gudanar da bukukuwan nune-nune da gasar wasannin motsa jiki da al'adu da sauransu. Ta ba da misali cewa, "Adadin tarukan kungiyoyin kasa da kasa da yankin Macao ya halarta ya karu daga 51 zuwa guda 120, lamarin da ya nuna cewa, yana ci gaba da habaka da zurfafa mu'amalarsa da katare. Tun bayan da yankin Macao ya dawo hannun kasar Sin, adadin kasashen da suka bai wa al'ummomin yankin Macao takardar biza kyauta ya karu daga kasashe 3 zuwa guda 144, yanzu haka al'ummomin yankin ta fita ketare ba tare da wata matsala ba. Kuma bikin cika shekaru 10 da gasar kacici-kacici ta matasa da yara game da harkokin diflomasiyya aka shirya, ya janyo hankula matasa da yara na yankin Macao da yawa. Bugu da kari, bikin bude hukumar wakilan ma'aikatar harkokin wajen Sin dake yankin Macao, da taron jakadu matasa da yara da wasu bukukuwan diflomasiya da aka shirya, sun karfafa ra'ayin kishin kasa na al'ummomin yankin Macao."

Daga bisani, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng ya bayyana cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da tsarin "kasa daya tsarin mulki biyu", domin kare "kundin tsarin mulkin kasa" da "babbar doka" yadda ya kamata, da nuna adawa da yadda kasashen ketare dake son tsoma baki a harkokin Macao da Hong Kong na kasar Sin, ta yadda za a kiyaye ikon mulkin kasa da tsaro da ci gaban kasar Sin, da kuma kiyaye zaman karko da bunkasuwar yankin musamman na Macao. A sa'i daya kuma, ya ce, za a dukufa wajen taimakawa yankin Macao ta yadda zai inganta rayuwar al'umma da tattalin arzikinsa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China