Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban yankin Sin da yankin Macao sun sanya hannu kan yarjejeniyar musayar kudi
2019-12-05 21:28:24        cri
Babban bankin kasar Sin PBOC, ya ce ya sanya hannu kan yarjejeniyar musayar kudi tare da hukumar kudin yankin musamman na Macao.

Sassan biyu dai sun amince da yin musayar kudin da yawan su ya kai kudin Sin yuan biliyan 30, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 4.3, da kudin Macao Patacas biliyan 35.

A cewar PBOC, wannan mataki na da nufin samar da daidaito a fannin hada hadar kudade, da tallafawa harkokin cinikayya da tattalin arziki ga sassan biyu. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China