Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An cafke mutane 62 da laifin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a Ghana
2019-12-15 16:29:39        cri
Yan sanda sun sanar a jiya Asabar cewa an kama mutane 62 da ake zarginsu da laifin hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a garin Kenyasi dake shiyyar yammacin kasar Ghana.

Matakin ya biyo bayan samun korafe-korafen da wani kamfanin hakar zinare na kasa da kasa mai suna Newmont Goldcorp, ya sha gabatarwa ne game da yawaitar masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba wadanda ke yin kutse a yankunan dake karkakashin ikon kamfanin a garin Kenyasi.

Kwaku Buadu Peprah, kwamandan hukumar 'yan sandan yankin wanda ya jagoranci aikin sintirin, ya ce sun yi nasarar damke masu hakar ma'adanan ba bisa ka'ida ba da misalin karfe 4 na safe wato daidai da karfe 4 na safe agogon GMT.

Wadanda ake zargin sun hada da mata biyu, kuma za'a gurfanar da su a ranar Litinin, inji jami'in.

A matsayinta na kasa mafi samar da zinare a Afrika, Ghana ta sha kaddamar da shirin yaki da masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba, inda hukumomin ke korafin cewa hakan yana haifar da gurbacewar ruwa a yankunan dake da arzikin ma'adanai a kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China