Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Ana fatan Amurka za ta daina nuna kiyaya ga sauran kasashe
2019-12-09 19:57:30        cri

Kwanan baya sakataren tsaron Amurka Mark Esper ya yi tsokacin da bai dace ba kan harkokin kasar Sin, yau Litinin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da nacewa kan hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, a sa'i daya kuma tana aiwatar da manufar tsaron kanta, kana tana fatan Amurka ta daina zargin sauran kasashe kamar yadda take so, kuma ta daina nuna kiyaya ga sauran kasashe.

Rahotanni na cewa, kwanan baya sakataren tsaron Amurka Mark Esper ya gabatar da wani jawabi, inda ya bayyana cewa, manyan kasashe kamar su Rasha da Sin suna neman nuna adawa da kudurorin da za a zartas da su kan tattalin arziki da tsaro na kananan kasashe, kan wannan batun Hua Chunying ta nuna cewa, Amurka ta gina sansanonin aikin soja sama da dari daya a wurare daban daban na fadin duniya, haka kuma tana matsa lamba ga wasu kasashe domin su yi watsi da 'yancinsu, a sanadin haka, Amurka ta jefa al'ummomin kasashen duniya da yawan gaske cikin mawuyacin hali.

Jami'ar ta jaddada cewa, har kullum kasar Sin tana aiwatar da manufar harkokin waje mai 'yancin kai, tana nacewa kan manufar daidai wa daida tsakanin daukacin kasashen duniya, manya ko kanana, kana kasar Sin ba ta taba tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran kasashe ba, sannan ba ta taba cin zalin wasu kasashe ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China