Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan Pompeo zai kauracewa zargin manufofin kasar
2019-11-18 20:25:34        cri

A yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi, a yau Litinin, kakakin ma'aiktar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, yanzu haka sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya sake furta wasu kalamai na zargi tsarin mulki da manufofin kasar Sin, sai dai kuma kasar Sin, na fatan jami'in zai kauracewa aikata hakan.

Jami'in ya ce, a cikin kwanakin da suka gabata, Pompeo yana ta sukar harkokin kasar Sin, domin shafawa kasar kashin kaji, amma fa a hakika zargin na sa ba shi da tushe, kuma ko kadan, Pompeo bai fahimci tarihi da yanayin kasar Sin ba.

Geng Shuang ya kara da cewa, kasar Sin tana sa ran Pompeo zai daina zargin ta, zai kuma daidaita huldar dake tsakanin Sin da Amurka ta hanyar daukan matakan da suka dace, ta yadda za a ingiza ci gaban huldar su cikin lumana.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China