![]() |
|
2019-11-21 19:45:41 cri |
Kakakin ma'aikatar cinikayyar kasar Sin Gao Feng, ya ce kasar sa ta himmantu, wajen ganin ta cimma matsaya a zango na farko, na yarjejeniyar cinikayya da take fatan cimmawa tsakanin ta da Amurka, ta yadda sassan biyu, da ma sauran sassan duniya za su amfana.
Gao Feng wanda ya bayyana aniyar kasar ta Sin, yayin taron manema labarai da ya gudana a Alhamis din nan, ya ce bangarorin biyu za su ci gaba da ganawa kai tsaye, domin tabbatar da nasarar da aka sanya gaba.
Ko da a ranar Asabar da ta gabata ma dai, manyan jami'an dake wakiltar sassan biyu a shawarwarin dake gudana, sun zanta da juna ta wayar tarho, inda suka fayyace abubuwan da kasashen su ke maida hankali a kan su, a gabar da ake tunkarar cimma matsaya a zango na farko na yarjejeniya. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China