Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar wajen Sin: Amurka ce ke kawo hadari ga kudancin tekun Sin
2019-11-19 20:42:37        cri

A kwanan baya ministan tsaron Amurka Mark T. Esper, ya yi ganawa da ministocin tsaron kasashen kungiyar ASEAN, inda ya zargi kasar Sin da yin barazana ga sauran kasashen dake yankin kudancin tekun kasar.

Kan wannan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana yau Talata a nan birnin Beijing cewa, aikin da Amurka ke gudanarwa a yankin, shi ne dalilin da ya sa yanayin da yankin ke ciki ke kara tsananta, kana Amurka tana fadin abun da bai dace ba kan huldar dake tsakanin kasashen dake cikin yankin, lamarin da ke kawo barazana ga kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin.

Geng Shuang ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan Amurka za ta kara fahimtar hakikanin yanayin da yankin ke ciki a halin yanzu, haka kuma ta girmama, da kuma goyon bayan kasashen, wajen kiyaye zaman lafiya a yankin, tare kuma da kauracewa daukar matakan da ba su dace ba. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China