Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A gaggauta kwantar da kura a Hong Kong
2019-11-26 21:09:51        cri

Yau kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin ya gabatar da wani sharhi, inda ya ce, kwanan baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da shirin doka kan hakkin dan Adam da harkokin dimokuradiyya a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin a shekarar 2019, lamarin da sassan daban daban na Hong Kong suka yi tir da shi. Yanzu haka abubuwan da suke faruwa a Hong Kong ba su da nasaba da batun kiyaye hakkin dan Adam da harkokin dimokuradiyya. Ya zama tilas a kawo karshen hankalin dake faruwa da dawo da doka da oda da tabbatar da aiwatar da doka cikin hanzari.

Sakamakon goyon baya daga gwamnatin tsakiyar kasar Sin da al'ummomin kasar da yawansu ya kai biliyan 1.4 da kuma kokarin da jama'ar Hong Kong da yawansu ya wuce miliyan 7 suke yi tare, ya sa tabbas za a kara karfin kwantar da kura a yankin, za kuma a sake samun kwanciyar hankali a yankin. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China