2019-12-07 15:48:23 cri |
A taron kasa da kasa na wuni biyu wanda aka kaddamar a ranar Juma'a a helkwatar kungiyar AU dake Addis Ababa na kasar Habasha, an kara jaddada yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afrika domin tabbatar da bunaksa shirin samar da dawwamamman cigaba.
A jawabinsa na bude taron, jakadan kasar Sin a AU, Liu Yuxi, ya nanata aniyar kasar Sin na cigaba da zurfafa hadin gwiwarta da yin hulda da Afrika don tabbatar da samun kyakkyawan sakamako karkashin tsarin mutunta juna da cin moriyar juna.
Wakilin ya ce, kasar Sin za ta cigaba da bayar da goyon baya da tallafawa Afrika a kokarin da nahiyar ke yi wajen fadada hanyoyin cigaban tattalin arziki, da bunkasa masana'antu, da inganta ayyuka a nahiyar, musamman wajen ba da fifiko game da raya cigaban tattalin arzikin nahiyar Afrika ta fannin aikin gona. (Ahmad Fagam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China