Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban CAR ya karrama masanan kasar Sin saboda kawo fahasar JUNCAO a kasar
2019-12-03 10:34:53        cri

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera (CAR) ya karrama masanan kasar Sin guda shida, bisa ga gudummawar da suka ba da a fanin aikin gonar kasar, ta hanyar fasahar shuka ciyaye da laimar kwadi (JUNCAO).

Shugaba Touadera, ya karrama wadannan masana guda shida da suka fito daga cibiyar aikin injiniya dake bincike fasahar JUNCAO a jami'ar aikin gona da gandun daji ta Fujian dake kasar Sin, a wani biki da aka shirya ranar Lahadi, yayin da kasar ke bikin cika shekaru 61 da kafuwa.

A jawabinsa yayin bikin shugaba Touadera, ya ce, al'ummar kasarsa ce a kullum ke fara amfana da hadin gwiwa da kasar Sin, yana mai imanin cewa fasahar, za ta samarwa kasar wata sabuwar hanya, a kokarin da take yi na kawar da talauci, samar da abinci da karin kudaden shigar jama'a.

Daga bisani, shugaban ya gwada laimar kwadin, yana mai cewa, an noma su ne bisa hadin gwiwa da kasar Sin.

A watan Maris din shekarar da ya gabata ce, Lin Zhanxi da tawagarsa suka yi tattaki zuwa kasar CAR don koyawa manoman kasar fasahar shuka ciyaye da laimar kwadi ta JUNCAO kyauta. Ana amfani da wannan fasaha ce wajen samar da laimar kwadi, abincin dabbobi da ma makamashi ta hanyar amfani da tsirrai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China