Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Matsalar tsaro ta kasance babban kalubalen dake damun bangaren makamashin Afirka
2019-12-05 09:29:39        cri
Majalisar kula da harkokin makamashin nahiyar Afirka (AEC) ta bukaci gwamnatoci da kamfanonin mai dake nahiyar, da su kara zage damtse don daukar matakan tsaron da suka dace, don kare bangaren makamashin nahiyar.

Majalisar dake birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, ta bayyana cikin wani rahoton nazari game da makamashin Afirka na shekarar 2020 na baya-bayan da ta fitar cewa, albarkatun mai da kayayyakin da ake sarrafawa daga man fetur, da danyen mai da iskar gas(LNG) da ragowar kayayyakin more rayuwa na zahiri dake da nasaba da makamashi, suna fuskantar matsalar tsaro a dukkan fadin duniya, musamman yankin yammacin Afirka.

Rahotanni na cewa, kasashen dake hako mai kamar Najeriya, na daga cikin kasashen dake fuskantar matsalar satar makamashi da lalata kayayyaki da matsalar 'yan fashin teku, abubuwan dake yin kafar ungulo ga tsaron makamashi, da ma tattalin arzikiin kasashen da suke dogara kwaca-kwam kan mai.

Majalisar AEC ta amince da wani shiri na hada kan manyan masu ruwa da tsaki da shugabannin tsaro daga masu gudanarwa, da tsarawa da kamfanonin hidima, don tattauna da ma magance manyan kalubaloli kamar garkuwa da mutane don neman kudin fansa, lalata bututan mai, satar danyen mai, tsaron tashoshi da hadin kan al'umma.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China